Crystal Palace za ta dauko Zaha

Wilfried Zaha
Image caption Zaha zai koma Palace ne a matsayin aro

Kulob din Crystal Palace na tattaunawa da dan wasan gefe Wilfried Zaha wanda zai koma kulob din daga Manchester United a matsayin aro.

Dan wasan mai shekaru 21, ya koma United daga Palace a watan Janairun 2013 kan kudi fam miliyan 15, ya kuma karasa wasannin kakar a kulob din a matsayin aro inda ya taimaka wa United samun nasara.

Ya buga wa Manchester wasanni hudu kadai daga bisani ya koma Cardiff a matsayin aro a karo na biyu a kakar.

Zaha na da kwallaye 18 a wasanni 143 da ya buga.