CAF ta ce ba karin sauya wurin wasa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Caf ta ce za ta sake nazari a kan lamarin a tsakiyar watan Satumba.

Hukumar harkokin kwallon Afirka CAF ta ce ba za a kara sauya tsarin wasannin samun cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na watan gobe ba, duk da bukatun sauya wuraren da za a yi karawar saboda fargabar cutar Ebola.

Caf ta bayyana a shafinta na intanet cewa: "Saliyo, Guinea da Liberiya ne kawai kasashen da ake bukata su sauya jadawalin wasansu zuwa kasashen da babu barazanar bullar Ebola."

Kasar Kamaru, ita ce ta baya-bayan nan da ta bayyana fargaba a kan cutar Ebola, inda ta bukaci a sauya wurin karawarsu da jamhuriyar Kongo.

Tun a farkon wannan wata, Hukumar kwallon Afirka ta fada wa Saliyo da Guinea cewa su sauya wuraren da za su karbi wasanninsu zuwa wasu kasashe, inda Guinea ta zabi yin wasanta da Togo ranar 5 ga watan gobe a Morocco.

Saliyo ma, da ta haramta dukkanin harkokin tamola a kasar daga ranar 4 ga wannan wata, har yanzu ba ta zabi kasar da za ta kai wasanta na ranar 10 ga watan gobe da Kongo ba.