Nigeria: Fifa ta yi watsi da zaben NFF

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fifa ta yi barazanar dakatar da Najeriya daga harkokin wasanni idan ta yi watsi da umarninta

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta yi watsi da zaben sabbin shugabannin hukumar kwallon kafa ta Nigeria, NFF inda ta umarce su, su fice daga ofis zuwa ranar Litinin.

Fifa ta dauki wannan mataki ne sakamakon rikicin da ake fama da shi a hukumar kwallon ta Najeriya, ta yadda aka gudanar da zaben shugabannin cikin rudani.

Kafin gudanar da zaben na shugabannin ne ranar Talata jami'an tsaron kasar suka tsare shugaban NFF din mai barin gado, Aminu Maigari, wanda ya kamata ya jagoranci babban taron da zai sanya ido kan zaben.

Bayan tsare shi ne kuma wasu wakilai a wurin taron suka gudanar da zaben, inda aka ce an zabi Christopher Giwa a matsayin sabon shugaban na NFF.

Rahotanni sun ce hukumar Fifa ta aike wa da babban sakataren kwallon kafar ta Najeriya takarda cewa, ba za ta amince da zaben da aka yi wa Mr Giwa da sauran shugabannin bangaren nasa ba, zaben da Fifan ta ce ma'aikatar wasanni ta Najeriyar ta amince da shi.

Haka kuma rahotanni sun ce sakamakon rikicin hukumar kwallon ta Najeriya, a yanzu an dakatar da gasar lig din kasar.

Karin bayani