Ana iya dakatar da ivory coast a kan Ebola

Hakkin mallakar hoto Associated Press
Image caption Caf ta ce a iya saninta za a buga wasan a Abidjan kamar yadda aka tsara

Ivory Coast ka iya fuskantar soke cancantarta ta zuwa gasar cin kofin Afirka a badi idan ta sarayar da wasan da za ta yi da Saliyo saboda fargabar daukar Ebola.

Gwamnatin Ivory Coast ta ce ba za ta bari a buga wasan ba, wanda aka tsara gudanarwa ranar 6 ga watan Satumba a birnin Abidjan.

Ivory Coast ta ce ba ta da zabi sai dai a kai karawar wata kasa daban ko kuma ta hakura.

Sai dai wani magana da CAF ya fada wa BBC cewa idan wata kasa ta sarayar da wasan samun cancanta guda daya, za a soke cancantarta ta zuwa gasar.

Saliyo na daya daga cikin kasashe shida masu fama da cutar Ebola, don haka gwamnatin Ivory Coast ke nuna damuwar cewa ana iya kai mata Ebola cikin kasar.