An dakatar da gasar Firimiyar Nijeriya

Image caption Rikicin shugabancin NFF ya janyo dakatar da Nijeriya daga harkokin wasanni a kwanan baya

Kwamitin shirya gasar Firimiya a Nijeriya ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan zaben shugaban Hukumar NFF mai cike da takaddama a ranar Talata wanda ya janyo rarrabuwar kai.

Kungiyar alkalan wasa ta kasar ta ce ta janye 'ya'yanta daga busa duka wasanni har sai an samu tsafta cikin harkar.

Jami'an da ke shirya gasar sun ce a yanzu, ba zai yiwu su ci gaba da gudanar da gasar ba.

Jami'in kwamitin shirya gasar Salihu Abubakar ya ce an sanar da kungiyoyi da abokan daukar nauyi, kuma an bukaci kulobluka su dakata har sai sun ji sanarwa.

Umarnin kungiyar alkalan wanda babban sakatarenta, Moroof Oyekunle Oluwa ya fitar na cewa matakin ya shafi gasar 'yan rukuni na 1, da wasannin cin kofin FA na Nijeriya da gasar Firimiya ta mata.