Ronaldo ne gwarzon dan wasan UEFA

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon dan Manchester ya ci kwallaye 51 a gasar daban-daban, yayin da Madrid ta zama zakara a Turai

Dan wasan gaba na Real Madrid Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Uefa a Turai, inda ya sha gaban 'yan wasan Bayern Munich biyu Manuel Neuer da Arjen Robben.

Kyaftin din na kasar Portugal mai shekaru 29, ya kafa tarihi inda ya ci kwallaye 17 don taimaka wa kungiyarsa Real Madrid lashe gasar zakarun Turai a kakar bara.

Ronaldo ya ce ya yi matukar farin ciki da wannan karramawa, ya ce jazaman ne ya yaba wa yan wasan kungiyarsa saboda ba don su ba, da bai samu kyautar gwarzon Uefa ba.

Mai tsaron gida Neuer, dan shekaru 28, ya taimaka wa Jamus lashe kofin duniya, shi kuma Robben mai shekaru 30, ya ci wa kungiyarsa Bayern Munich kwallaye 21, ya kuma ci wa kasarsa Holland kwallaye uku a kan hanyarsu ta zuwa wasan kusa da na karshe a Brazil.

Ronaldo wanda bai taka wa kasarsa rawar a-zo-a-gani ba a gasar cin duniya, inda aka cire ta a zagayen rukuni, sai dai kwazon da ya yi wa kulob dinsa Madrid ya ja hankalin masu zabe da suka kada masa rinjayen kuri'u.

Tsoffin gwarazan 'yan wasan Uefa a Turai

2010-11 Lionel Messi (Barcelona) 2011-12 Andres Iniesta (Barcelona) 2012-13 Franck Ribery (Bayern Munich)