Wenger ya ce zai sayi karin 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger ya ce samun nasara a kakar wasanni ba ta dogara a kan wani dan wasa da ka saya, ko ba ka saya ba

Kocin Arsenal Wenger ya ce kungiya tana iya yin zaben tumun dare a ranakun karshe kafin rufe damar sayen 'yan wasa a litinin din makon gobe.

Ya ce zai shiga kasuwar sayen 'yan wasa har a ranar karshe ta wannan dama, ya kara da cewa kungiyoyi da dama suna shiga kasuwar kuma lamari ne na kar-ta-san-kar.

Wenger ya zuba fam miliyan 42.5 a kakar bara don sayen dan wasan tsakiya na kasar Jamus Mesut Ozil ya kuma a shirye suke a ko yaushe su kashe kudi wajen sayen dan wasa na kwarai.

Ya ce akwai karairayi sosai a ranakun karshe, za a ce ma akwai kungiyoyi da dama da ke neman dan wasa, ko da kuwa kai kadai kake son daukarsa.

Arsene Wenger, wanda kungiyarsa ta bakunci Leicester City da ta hau Firimiya a lahadin nan, ya ce yana da 'yan wasan gaba da dama da za su maye gurbin Olivier Giroud da aka yi wa dorin karaya.