Chelsea ta kammala daukar Remy

Loic Remy Hakkin mallakar hoto chelsea fc
Image caption Remy ya ce zai buga wasa tukuru a Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala daukar dan wasan Queens Park Rangers Loic Remy kan kwantiragin shekaru hudu kan kudi sama da fam miliyan 10.

Chelsea ta biya kudin yarjejeniyar dan wasan ne a tsakar ranar Asabar, kuma nan take QPR ta cire sunansa daga 'yan wasan da za su kara da Sunderland a ranar.

Remy mai shekaru 27 dan kwallon Faransa ya ce "Na kasan ce cikin farin ciki da tunkaho tun lokacin da Chelsea suka fara zawarci na, kuma tuni na amince na koma kulob din".

Itama Arsenal ta nuna sha'awar dauko dan kwallon a daren Asabar, lokacin da tuni Chelsea ta amince da daukar dan wasan.