Van Ginkel ya koma AC Milan wasa aro

Marco van Ginkel Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasa na biyu daga Chelsea da ya koma Milan

Dan kwallon Chelsea Marco van Ginkel ya koma kulob din AC Milan ta Italiya wasa aro na kakar wasa daya.

Mai shekaru 21 da haihuwa dan kwallon Netherlands ya koma Chelsea daga Vitesse Arnhem kan kudi fam miliyan 8 a watan Yulin shekarar 2013, amma wasanni hudu ya buga wa kulob din.

Van Ginkel ya ce "Milan babbar kungiya ce a Turai, kuma zan samu damar buga wasanni a kulob din a gasar Seria A da manyan kungiyoyi da zakakuran 'yan wasa.

Shi ne dan kwallo na biyu daga Chelsea da ya koma wasa Milan, bayan da Fernando Torres ya koma kungiyar wasa aro na tsawon shekaru biyu.