Beckham bai so Welbeck ya bar United

David Beckham Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Beckham ya ce ya kamata a karfafa 'yan wasan Ingila gwiwa

David Beckham ya ce bai ji dadi da Danny Welbeck ya bar kulob din Manchester United ba, amma yana da yakinin zai taka rawa a Arsenal.

Welbeck ya fara buga wa United tamaula tun yana matashin dan wasa, ya kuma koma Arsenal kan kudi fam miliyan 16 ranar karshen rufe kasuwar musayar 'yan kwallon Turai.

Beckham tsohon dan kwallon United ya ce "Kulob din Arsenal yana da matasan 'yan wasan Ingila kuma zakakurai".

"Na yi bakin cikin barinsa United domin ya fara buga mata tamaula tun yana da shekaru takwas, kuma hakika zuciyar Welbeck tana kaunar kulob din".

Welbeck ya fara wasa a United a shekarar 2008, ya kuma buga wasannin Premier 53 da kuma wasanni 39 da ya yi canji.

Dan wasan ya rasa gurbinsa bayan da kulob din ya dauko Radamel Falcao da Angel Di Maria, sannan ga Rooney da Robin van Persie suna kan ganiyarsu.