Nigeria za ta fuskanci fushin FIFA

NFF Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption NFF na fama da rikici, da ke neman kawo mata koma baya

Nigeria za ta fuskanci fushin Fifa, bayan da Chris Giwa ya ki sauka daga kujerar shugabancin hukumar kwallon kafar kasar NFF, duk da wa'adin data bayar ranar Litinin da ya wuce.

Idan har Fifa ta dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa, zai shafi wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka domin kare kambunta.

Fifa ta ki amincewa da zaben Giwa, inda ta umarci da ya bar ofishin hukumar kafin daren Litinin da ta gabata.

Sai dai FIFA ta amince da taron mambobin hukumar su 39 daga cikin 44 da suka zartar da cewa ranar 4 ga watan Satumba a gudanar da sabon zaben hukumar.

Sau biyu FIFA tana shiga tsakanin rigimar hukumar NFF, lokacin da wata kotu ta sauke Aminu Maigari da kuma dakatarwar da kwamitin amintattun hukumar ya yi masa.