Obiazor zai maye gurbin Enyeama

Stephen Keshi
Image caption Kocin na sauraren sauran 'yan wasa da za su ziyarci sansani

Kocin Super Eagles Stephen Keshi, ya maye gurbin Vincent Enyeama da golan Elkanemi David Obiazor wanda zai tsare raga a karawar da kasar za ta yi da Congo ranar Asabar.

Tuni sansanin horon 'yan wasan Super Eagles dake jihar Calaba ya kara tumbatsa, a shirin da suke na karawa da Congo a wasan share fagen shiga gasar kofin Nahiyar Afirka na badi a Morocco.

Koci Stephen Keshi da mataimakansa sun karbi bakuncin 'yan wasa da suka hada da Ahmed Musa da Ogenyi Onazi da Efe Ambrose da Kenneth Omeruo da Juwon Oshaniwa da Sone Aluko da John Mikel Obi da kuma Austin Ejide da tsakar ranar Talata.

Keshi ya ce ya yi farin ciki da yadda 'yan wasa suka amsa kira, kuma yana sa ran halartar sauran 'yan kwallon nan ba da dadewa ba.

Nigeria zakarar kofin Nahiyar Afirka za ta karbi bakuncin Congo kafin ta ziyarci Afirka ta Kudu kwanaki hudu tsakani.