FIFA ta ba NFF wa'adin maida Maigari

Chris Giwa
Image caption FIFA ta bai wa Nigeria nan da ranar Litinin ko ta fuskanci hukunci

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta baiwa hukumar kwallon kafar Nigeria NFF wa'adin sauke Chris Giwa daga kujerar shugabancin NFF tare kuma da mayar da Aminu Maigari kan kujerar nan da ranar Litinin ko kuma ta fuskanci hukunci.

Cikin hukuncin da FIFA za ta iya dauka har da dakatar da Nigeria daga shiga harkar wasan kwallon kafa, da zai iya kawo barazana ga wasan neman tikitin shiga kofin Nahiyar Afirka da Najeriyar ke nema inda za ta kara da Afirka ta Kudu a birnin Cape Town.

FIFA ta ce ba ta yarda da zaben da aka gudanar ranar 26 ga watan August ba, wanda Giwa ya dare kan kujerar hukumar NFF.

Haka kuma hukumar tace a maida Aminu Maigari kan kujerarsa, sannan a shirya yadda za a gudanar da zaben sababbin shugabannin NFF din.

FIFA ta bada wa'adin karshe ne ga Nigeria, bayan wani taron gaggawa da ta gudanar kan kin saukar Giwa daga kujerar shugabancin NFF bayan da a baya ta bada wa'adin ya sauka kan kujerar ranar 1 ga watan Satumba.

Ko a wannan shekarar an dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa kwanaki tara a watan Yulin da ya gabata, bayan da gwamnati ta tsoma baki a harkar kwallon kafar kasar.