Uche: Sai Nigeria ta roke ni yin wasa

Ikechuku Uche
Image caption Dan wasan ya nemi da Keshi ya roke shi kafin ya buga wa Nigeria wasa

Dan wasan Nigeria Ikechuku Uche ya ce sai Stephen Keshi ya roke shi, kafin ya dawo buga wa Super Eagles tamaula.

Nigeria za ta kara da Congo a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, wanda ta gayyato yan kwallo 23 da za su buga mata wasan amma babu Uche a ciki.

Keshi bai gayyaci dan kwallon zuwa gasar cin kofin duniya da aka kammala a Brazil ba, inda kocin ya ce dan wasan ba shi da da'a.

Tuni dai sansanin Super Eagles da ke Calaba ya bunkasa, wanda ragowar 'yan wasa biyun da ake jira Emmanuel Emenike da Joel Obi suka isa.

Sai dai golan El Kanemi David Obiaozor wanda zai maye gurbin Enyeama a raga har yanzu bai samu damar isa ba.

Keshi ya ce Uche yana cikin jerin 'yan wasan da yake sa ran gayyata tawagar kasar don kare kambunta, amma babu wani dan wasa da zai roka ya buga wa Nigeria tamaula.