AFCON 2015: Za a fara wasanni Juma'a

AFCON 2015 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe 15 ne za su nemi tikiti don hadewa da mai masaukin baki Morocco

Kasashe 28 ne za su fara wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka ranar Juma'a domin fidda 15 da za su fafata a badi da Morocco za ta karbi bakunci.

Wasu wasannin sun gamu da cikas inda aka sauya filin wasa a kokarin kaucewa kamuwa da kwayar cutar Ebola.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta umarci dauke wasa tsakanin Guinea da Saliyo zuwa wani filin wasa daban, saboda cutar Ebola da ta barke a kasashen biyu.

Wasannin da za a fafata ranar Juma'a sun hada da karawar farko da za a yi tsakanin Sudan da Afirka ta Kudu, yayinda Guinea za ta karbi bakuncin Togo a Casablanca da kuma karawa tsakanin Senegal da Masar.

Ranar Asabar Ghana za ta karbi bakuncin Uganda a Kumasi, inda mai rike da kofin Nigeria za ta kara da Congo a Calaba duk da dakatarwa da take fuskanta daga FIFA.

Ga wasannin da za a kara ranar Asabar

Jamhuriyar Congo vs Cameroon Ethiopia vs Algeria Zambia vs Mozambique Niger vs Cape Verde Burkina Faso vs Lesotho Gabon vs Angola Ivory Coast vs Saliyo Mali vs Malawi Tunisia vs Botswana