Brazil za ta kara da Colombia

Brazil Dunga Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Dunga na shirin dawo da tagomashin Brazil

Sabon kocin Brazil Dunga ya bukaci 'yan wasan tawagar kasar da su mance da rashin kokarin da suka yi a gasar kofin duniya su fuskanci kalu balen da ke gabansu.

Kocin mai shekaru 50, wanda ya taba horas da kasar a shekarun 2006 da 2010 ya maye gurbin Luiz Felipe Scolari tun a watan Yuli.

Brazil za ta kara da Colombia a wasan sada zumunci wanda za su kara a Miami ranar Asabar.

Wannan shi ne karon farko da kasar za ta buga wasa tun lokacin da Netherlands ta doke ta da ci 3-0 a gasar kofin duniya ranar 12 ga watan Yuli.

Cikin nasarar da kocin ya samu a karon farko da ya horas da kasar ya lashe kofin Amurka bayan da suka doke Argentina da ci 3-0 a wasan karshe.