Golan Stoke City Begovic ya kafa tarihi

Asmir Begovic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Begovic ya ce ya ji dadin kafa tarihin da ya yi

Golan Stoke City Asmir Begovic ya shiga kundin tarihin Guinness World Records a dan wasan da ya ci kwallo daga nesa.

Begovic mai shekaru 27 ya zura kwallo ne a ragar Southampton a wasan da suka tashi kunnen doki a watan Nuwambar bara.

Kwallon da ya buga ta yi tafiyar dakika 13 a sararin sama, kafin ta wuce mai tsaron raga Artur Boruc ta kuma fada raga.

Bayan da aka gwada tafiyar kwallon zuwa raga ya kai mita 91.9 daidai da kafa 301 da inci 6, dalilin da yasa ya kafa tarihi.

Begovic ya shiga sawun masu tsaron raga a gasar Premier da suka zura kwallo a raga da suka hada da Peter Schmeichel da Brad Friedel da Paul Robinson da kuma Tim Howard