Hodgson ya kare kokarin 'yan wasansa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ya ce ba batun kididdiga ba ne, 'yan wasan ingila sun mamaye wasan

Kocin Ingila Roy Hodgson ya kare matsayinsa na yin sukar mutanen da suka zargi 'yan wasansa da rashin tabuka abin a-zo-a-gani yayin karawarsu da Norway.

Hodgson ya maida martani cikin fushi game da batun da wasu ke yi cewa sau biyu kawai Ingila ta kai hari a ragar abokiyar karawarta, ciki har da bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda Wayne Rooney ya yi nasarar ci aka tashi wasa 1 da nema.

Da aka tambaye shi game da kaduwar da ya nuna, Kocin ya ce "ka ga, mene ne laifina?" Idan aka tunkare ka da tambayar cewa kwakkwaran hari sau biyu kawai 'yan wasanka suka yi.

A ranar Litinin mai zuwa ne Ingila za ta kara da Switzerland, a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin kasashen Turai a 2016.

Kocin mai shekaru 67, ya nuna bacin rai bayan wasan sada zumuncin da kungiyarsa ta buga a gaban 'yan kallo 40,181, a kokarinsa na kare kwazon 'yan wasansa.