Zlatan ne gwarzon dan wasan Sweden

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ya ce kwallon da ya ci Ingila a 2012, ita ce mafi burgewa a kwallayen 50

Dan wasan Paris St-Germain Ibrahimovic ya zama dan kasar Sweden mafi ci mata kwallo a tarihi bayan karawarsu da Estonia.

Zlatan Ibrahimovic ya zama dan wasa mafi cin kwallaye a tarihin kasar Sweden ne bayan jefa wa Estonia kwallaye biyu a karawarsu ta jiya.

Dan wasan mai shekaru 32 ya ci kwallon farko ne a wasan, minti uku kacal da take leda sakamakon wani bugun kwana da aka dauko.

Ibrahimovic wanda ya buga wa Sweden wasanni 99, ya ci mata kwallonsa ta hamsin a minti na 24, aka tashi wasa 2 da nema.

Dan wasan ya karya tarihin Sven Rydell mai kwallaye 49 tun a 1932, tun da farko, tsohon dan wasan Ajax din da Juventus, Inter Milan da Barcelona, ya yi wasu-wasin buga wasan saboda ciwon makogwaro.

'Yan kallo 15,421 ne suka mike suna tafa masa a lokacin da yake fita daga fili bayan an yi canjinsa