Bai kamata a Kaurace wa Rasha 2018 ba

Hakkin mallakar hoto reuter
Image caption Shugaban Fifa ya ce Hukumar ba za ta kwace damar da ta bai wa Rasha ba.

Tsohon Ministan wasannin Burtaniya Richard Caborn ya ce kaurace wa gasar cin kofin duniya na shekara ta 2018 a Rasha, mai da hannun kyauta baya ne.

An ruwaito cewa jami'an tarayyar Turai suna tunanin fara yin kira ga kasashe don su kaurace wa gasar a matsayin wani matakin bijire wa ayyukan Rasha a Ukraine.

Richard Caborn ya ba da misali da gasar Olympics a birnin Moscow ta 1980, lokacin da Amurka ta ki halarta amma 'yan wasan Burtaniya suka shiga.

Tsohon mai shekaru 70 ya ce matakin zai kare ne kawai ga janyo rarrabuwar kan duniya, ya ce "ka ga an yi ba a yi ba kenan."

Caborn, wanda ministan wasanni ne tsakanin shekara ta 2001 zuwa 2007, jagora ne wajen neman kaurace wa harkokin wasannin Afirka ta kudu a lokacin mulkin wariyar launin fata, sai dai ya yi imani cewa irin wannan mataki a kan Rasha ba zai tsinana komai ba.