Ba Sturridge a wasan zuwa Euro 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hodgson na da zabin Rooney da Rickie Lambert da kuma Welbeck, idan ba Sturridge.

An kai dan wasan gaba na Ingila, Daniel Sturridge asibiti, don daukar hoton kafarsa bayan ya ji rauni a lokacin atisaye ranar Juma'a.

Ko da yake, ba a bayyana tsananin raunin da ya ji ba, amma dai likitoci za su tantance hoton kafarsa da za a dauka.

Dan wasan gaban na Liverpool mai shakaru 25, ya buga wasan sada zumunci da Ingila ta cinye Norway 1-0 har zuwa minti na 89 ranar laraba a filin wasa na Wembley.

A ranar Litinin ne 'yan wasan na Roy Hodgson za su fafata da Switzerland a wasan shiga gasar cin kofin Turai ta 2016 a Basel.

Sturridge wanda ya ci kwallaye biyar a wasanni 16 da ya buga wa Ingila, ya bar ayarin kungiyarsa Liverpool lokacin da take rangadin Amurka bayan ya samu cirar nama a kafarsa.