Jamus ta doke Scotland da ci 2-1

Germany VS Scotland Hakkin mallakar hoto sns
Image caption Jamus ta fara wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da kafar dama

Kasar Jamus ta doke Scotland da ci 2-1 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da su ka kara ranar Lahadi.

Jamus ce ta fara zura kwallo a ragar Scotland ta hannun dan wasanta Müller a mintuna na 18 da fara tamaula.

Scotland ta farke kwallonta ta hannun Anya a mintuna na 66, kafin daga baya Müller ya kara kwallo ta biyu cikin minti hudu tsakanin farke kwallon da Scotland ta yi.

Sai dai an kori dan wasan Scotland Charlie Mulgrew daga fili bayan da aka bashi jan kati.

Jamus tana rukuni na hudu tare da Poland da Ireland da Georgia da kuma Gibraltar.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Georgia 1 - 2 Jamhuriyar Ireland Hungary 1 - 2 Northern Ireland Gibraltar 0 - 7 Poland Tsibirin Faroe 1 - 3 Finland Greece 0 - 1 Romania Denmark 2 - 1 Armenia Portugal 0 - 1 Albania