Ronaldinho ya koma Queretaro

Ronaldinho Brazil Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya ce ya zabi kulob din domin ya bada gudunmawar da baza a manta da shi ba

Tsohon dan kwallon Brazil Ronaldinho ya koma kulob din Queretaro ta kasar Mexico kan kwantiragin shekaru biyu.

Dan wasan wanda ya lashe kofin duniya da Brazil a shekarar 2002, ya bar kulob din Atletico Mineiro da ke Brazil a watan Yulin da ya gabata.

Shima kulob din Basingstoke Town ya ce ya yi jawarcin dan kwallon wanda ya buga wa Brazil wasanni 97.

Queretaro yana matsayi na takwas a cikin wasannin cike gurbin gasar Liga MX ta bana bayan buga wasanni bakwai.

Ronaldinho ya lashe kofin zakarun Turai da Barcelona a shekarar 2006, ya kuma buga wa Paris St-Germain da kuma AC Milan, ya kuma lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar 2005.