Rooney na fargabar wasan Switzerland

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ingila za ta kara da Switzerland ranar Litinin

Kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya ce za su kai ruwa rana a karawar da za su buga da Switzerland a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai.

Kasashen biyu za su fafata a wasan farko cikin rukuni ranar Litinin, kuma ana hasashe cewa su biyu ne za su fito daga rukunin da ya kunshi Slovenia da Estonia da Lithuania da kuma San Marino.

Rooney mai shekaru 28 ya ce yana da kyau su fara lashe wasan farko domin shi ne zai fara auna makomarsu a neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai.

Ingila wadda ta ke matsayi na 11 a jerin kasashen da su kafi iya taka leda a duniya, za ta buga wasanne babu Daniel Sturridge saboda yana jinyar rauni.

Shima golan Ingila Ben Foster da Jack Colback suna jinyar rauni ba za su buga karawar ba ranar Litinin.

Ingila ta doke Norway da ci 1-0 a wasan sada zumunci a Wembley.