FIFA za ta yi amfani da TV kan hukunci

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Blater zai sake tsayawa zabe a shekarar 2015

Shugaban hukumar kwallon kafa na duniya Sepp Blatter ya ce za a yi amfani da talabijin domin bai wa kociyoyi damar kalubalantar hukunci wasa.

Blatter, mai shekaru 78, dan kasar Switzerland ya fadi hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi ta wata kafar yada labarai.

Ya kuma kara da cewa mai horas da wasa zai iya kalubalantar hukuncin wasa ne sau daya ko kuma sau biyu bayan an tafi hutun rabin lokaci.

Haka kuma ya ce za'a gwada sabon tsarin ne a gasar cin kofin duniya na mata masu shekaru kasa da 20 ta badi.

Haka kuma Blatter ya sanar da cewar zai sake tsayawa zabe a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa na duniya a shekarar 2015.