An warware takaddama a NFF

Image caption Aminu Maigari ya koma kan kujerarsa

Hukumar kwallon Nigeria ta warware takaddamar shugabancin da ta dabaibaye ta domin kauce wa hukuncin Fifa.

Chris Giwa ya sauka daga kujerar shugabancin NFF bayan da Fifa ta ba shi wa'adin ya sauka daga kujerar saboda babu hallaci a zabensa da aka yi.

A makon jiya ne Fifa ta jaddada cewa, ba ta amince da zabensa na ranar 26 ga watan Agusta ba.

Sakatare Janar na NFF, Musa Amadu ya shaidawa BBC cewar, "An warware matsalar kuma tuni ya koma bakin aikinsa."

Da Chris Giwa bai sauka ba, to da Fifa ta dakatar da Nigeria kuma hakan zai iya hana Super Eagles buga wasan share fage tsakaninta da Afrika ta Kudu domin neman halartar gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a shekara ta 2015.