FIFA ta ja kunnen NFF kan zabe

FIFA Logo Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption FIFA ta bukaci NFF ta shirya sabon zabe da gaggawa

FIFA ta rubuta wa hukumar kwallon kafar Nigeria NFF cewa ba a dakatar da Nigeria shiga harkar kwallon kafa ba, tun da ta cika ka'ida.

Tun a ranar 3 ga watan Satumba FIFA ta bai wa Chris Giwa wa'adin ya bar shelkwatar NFF ko kuma a hukunta Nigeria.

Hukumar ta FIFA ta kuma bukaci da abar Sakatare Janar na hukumar NFF Musa Ahmadu ya gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba.

NFF ta rubuta wa FIFA inda ta tabbatar mata da cewa za ta bi dukkan sharrudan da ta bata domin ciyar da wasan kwallon kafa gaba a Nigeria.

A cikin kunshin wasikar FIFA ta umarci da kwamintin amintattu na NFF ya tsara yadda za a gudanar da sabon zabe da kuma bai wa kowa damar tsaya wa takara.

FIFA ta ja kunnen Nigeria cewa kada wani abu ya kawo wa zaben tsaiko, kuma za ta shaida yadda za a gudanar da zaben sabbin shugabannin NFF.