Italiya ta doke Norway har gida da ci 2-0

Italia Win Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Italiya ta fara wasa da kafar dama domin neman tikiti

Kasar Italiya ta doke Norway da ci biyu da nema har gida a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Turai da suka kara ranar Talata.

Italiya ta zura kwallon farko ta hannun dan wasanta Zaza a minti na 16 da fara tamaula, kafin ta kara kwallo ta biyu ta hannun Bonucci a mintuna na 62.

Nasarar da Italiya ta samu yasa ta dare matsayi na daya wanda ya kunshi kasashe da suka hada da Croatia da Bulgaria da Azerbaijan da kuma Norway.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Netherlands ta yi rashin nasara a hannun Jamhuriyar Czech da ci 2 - 1.

Ga sauran sakamakon wasannin da aka buga:

Andorra 1 - 2 Wales Kazakhstan 0 - 0 Latvia Iceland 3 - 0 Turkey Bos-Herce 1 - 2 Cyprus Azerbaijan 1 - 2 Bulgaria Croatia 2 - 0 Malta