AFCON 2015: Kamaru ta casa Ivory Coast 4-1

Vincent Aboubakar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamaru ta lashe wasanni biyu a jere kenan

Kasar Kamaru ta doke Ivory Coast da ci 4-1 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka a karawar da su kayi a Yaounde.

Kamaru ta zura kwallaye hudu ne ta hannun 'yan wasanta Vincent Aboubakar da Clinton Njie wanda dukkansu suka zura kwallaye biyu a raga.

Ivory Coast ta zura kwallonta tilo a ragar Kamaru ta hannun Yaya Toure a minti na 10 da fara tamaula.

Kamaru ta lashe wasanni biyu kenan a rukuni na hudu, bayan da ta fara doke Jamhuriyar Congo a makon da ya gabata.

Wasu daga cikin sakamakon wasan da aka kara Saliyo ta sha kashi a hannun Congo har gida da ci 2-0, Malawi ta doke Ethiopia da ci 3-2, Congo Brazaville ta lashe Sudan da ci biyu da nema.