Suarez zai dawo tamaula a wasan Madrid

Luis Suarez Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Suarez zai fara buga wa Barcelona kwallo a karawa da Madrid

Kulob din Barcelona ya ce Luis Suarez zai fara buga wasan farko a kungiyar lokacin da za su kara da Real Madrid a gasar cin kofin La Liga ranar 25 ga watan Oktoba.

Wasan za a buga shi ne lokacin da dan wasan ya kara kwana daya kan hukuncin da aka yanke masa na dakatar da shi buga wasan tamaula saboda samunsa da laifin cizon Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya.

Hukumar kwallon kafa ta Spaniya (LFP) ce ta tabbatar da ranar da za a kara tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar Laraba.

Ita ma kotun daukaka karar wasanni (CAS) ta jaddada wa Barcelona cewar Suarez mai shekaru 27 da haihuwa zai iya buga wa kulob din wasan.

A wani jawabi da ta fitar ta intanet ta ce "dakatarwar da aka yi wa dan wasan na Uruguay za ta kare a daren ranar Juma'ar 24 ga watan Oktoba.