Afirka ta Kudu da Nigeria sun tashi 0-0

Super Eagles
Image caption Nigeria tana da maki daya bayan buga wasanni biyu

Nigeria ta riko canjaras a Afirka ta Kudu a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka da suka fafata a a filin wasa na Greenpoint ranar Laraba.

Kafin karawar kocin Nigeriya Stephen Keshi ya bugi kirjin cewar wasan tamkar gasar kofin duniya za su buga fafatawar.

Afirka ta Kudu ta buga karawar da karfin gwiwar lashe wasan ganin yadda ta doke Sudan har gida da ci 3-0, yayin da Congo Brazaville ta doke Nigeria har gida da ci 3-2.

Congo Brazaville tana matsayi na na daya da maki 6, bayan da ta doke Sudan da ci 2-0 a rukunin farko, Afirka ta Kudu na matsayi na biyu da maki uku sai Nigeria da maki daya a mataki na uku, inda Sudan ce ta karshe da rashin maki.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga:

Malawi 3-2 Ethiopia Angola 0-3 Burkina Faso Lesotho 1-1 Gabon Cameroon 4-1 Ivory Coast Sierra Leone 0-2 DR Congo Togo 2-3 Ghana Uganda 2-0 Guinea Mozambique 1-1 Niger Cape Verde 2-1 Zambia Botswana 0-2 Senegal Egypt 0-1 Tunisia