Bani da tabbas kan Super Eagles - Keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta buga wasanni biyu a jere babu nasara

Kocin Nigeria, Stephen Keshi ya ce bashi da tabbas a kan makomarsa ta ci gaba da jan ragamar tawagar Super Eagles.

Kwantiragin Keshi da Nigeria ya kare ne bayan kamalla gasar cin kofin duniya a Brazil, amma aka bashi damar ya jagoranci Super Eagles a wasanni biyu na share fagen neman buga gasar cin kofin Afrika da za a yi a Morocco.

A cewar Keshi, idan har aka sabunta masa kwantiragin da ya amince da ita, zai ci gaba da jagorantar Super Eagles idan ba haka zai tafi.

Saboda rikicin shugabanci a hukumar kwallon Nigeria-NFF, kawo yanzu ba a warware batun wanda zai zama kocin Super Eagles ba.

Nigeria na da wasanni biyu tsakaninta da Sudan a watan Oktoba, kuma kawo yanzu ta sha kashi a hannu Congo a birnin Calabar, sannan kuma ta tashi canjaras tsakaninta da Afrika ta Kudu a Cape Town.