Rodgers ya yi bakin cikin jin raunin Sturridge

Daniel Sturridge Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sturridge zai yi jinyar rauni tsawon makwanni uku

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya soki Ingila da yin wasa-rai-rai da Daniel Sturridge tun lokacin da dan kwallon ya ji rauni da zai yi jinyar makwanni uku.

Sturridge, mai shekaru 25, ya ji rauni ne lokacin da ya ke atisaye da tawagar Ingila a makon da ya gabata, wanda bai samu buga karawar da Ingila ta doke Switzerland da ci 2-0 ba ranar Litinin.

Rodgers ya ce "Mun yi bakin ciki matuka da jin labarin raunin Sturridge, kuma rauni ne da za a iya kauce masa".

Sturridge wanda ya buga wa Liverpool daukacin wasanni uku da ta buga a gasar Premier bana, ya buga wasan minti 89 a karawar da Ingila ta yi da Norway a Wembley ranar 3 ga watan Satumba.

Ya kuma ji raunin ne a lokacin da tawagar Ingila ke atisaye awonni 36 bayan kammala wasan sada zumunci a Wembley da Ingila ta lashe wasan da ci 1-0.