Welbeck ba ya cin kwallaye sosai - Van Gaal

Louis Van Gaal Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Falcao da Blind sabbin 'yan wasan da United ta sayo

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce sun sayar da Danny Welbeck ne saboda ba ya cin kwallo kamar yadda ya kamata.

Van Gaal ya sanar da hakan ne lokacin da yake kaddamar da sabbin 'yan kwallon da kungiyar ta dauko Radamel Falcao da Daley Blind gaban 'yan jaridu.

United ta sayar da Welbeck mai shekaru 23 kan kudi fam miliyan 16 ga kungiyar Arsenal wadda suke hamayya a Ingila.

Van Gaal ya ce "Welbeck ya buga kakar wasanni uku a jere, amma bai zura kwallaye a raga da suka kai yawan na Rooney ko Van Persie ba".

"Tunda mun dauko Falcao ya kamata Welbeck ya koma wata kungiyar domin ya gwada sa'ar shi, kuma wannan shi ne tsarin United.

Welbeck wanda ya zura wa Ingila kwallaye biyun da ta doke Switzerland ya zura kwallaye 29 a wasanni 142 da ya buga wa United.

Wayne Rooney, mai shekaru 28, ya zura kwallaye 217 cikin wasanni 445 da ya buga wa United, wanda Van Persie ya zura kwallaye 48 cikin wasa 78 da ya buga.

United ta kashe sama da fam miliyan 150 wajen sayo 'yan wasa a bana, sannan ta bar 'yan wasanta da dama sun bar kungiyar.