Aro na so na dauko Welbeck — Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya ce aro ya kamata ya dauko Danny Welbeck

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce da yana cikin Ingila ranar da aka rufe kasuwar musayar 'yan kwallo ba zai sayi Danny Welbeck ba.

Welbeck mai shekaru 23 ya bar Manchester United kulob din da ya fara buga tamaula tun yana yaro, ya kuma koma Arsenal kan kudi fam miliyan 16 lokacin da Wenger ya tafi Rome ta kasar Faransa.

Wenger ya ce da yana Ingila da Welbeck bai dawo Arsenal ba, duk da bai yi cikakken bayani akan abinda yake nufi ba, ya ce zai dauko dan wasan ne aro da sharadin sayansa daga baya idan ya taka rawa.

Kocin ya ce ya yi murnar daukar dan wasan zuwa Arsenal kacokan, sai dai bai bada tabbacin ko zai yi amfani da dan kwallon a karawar da za suyi da Manchester City ranar Asabar ba.

Arsenal za ta kara da Manchester City a gasar cin kofin Premier wasan mako na hudu a Emirates ranar Asabar.