Morocco 2015: Niger ba ta karaya ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Niger ta halarci gasar cin kofin Afrika a 2013

Kocin tawagar kwallon kafa ta Niger, Gernot Rohr na da kyakkyawan fatan cewa kasar za ta samu shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekara mai zuwa, duk da rashin fara wasannin rukuni da kafar dama da ta yi.

Niger ta sha kashi a wasanta na farko, na biyu kuma ta yi canjaras a kan hanyar zuwa gasar cin kofin Afirka a Morocco.

Niger tana can a kasan jadawalin rukunin F, bayan Cape Verde ta lallasa ta da ci 3-1 ranar 6 ga wannan wata, sannan kuma suka tashi kunnen doki 1-1 da Mozambique ranar laraba.

Kocin ya ce ko da yake ba su fara da wasanninsu da kafar dama ba, amma yana da kyakkyawan fatan Nijar za ta kai bantenta.

Ya ce ya yi farin ciki da sakamakon wasan da suka yi da Mozambique, ya ce ba abu ne mai sauki ga kungiyar ba ta farke kwallon da aka jefa mata a farkon wasa.

Gernot Rohr ya ce yana bai wa tawagar kaso sittin cikin 100 na yiwuwar zuwa Morocco 2015