Atletico ta casa Real Madrid

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau takwas ke nan Real ba ta ci Atletico a gida a La Liga ba

Abokan hamayyar Real Madrid na gida Atletico Madrid sun casa Zakarun Turan da ci 2-1 a Bernabeu.

Zakarun na La Liga sun fara jefa kwallo a ragar Real inda Tiago ya jefa kwallon raga da ka miniti 10 da shiga fili.

Cristiano Ronaldo, wanda ya dawo daga jiyya, ya rama da fanareti, a minti na 26.

Sai dai kuma 'yan Atletico wadanda suka jure matsi da hare-haren Real sun kara kwallo ta biyu ta hannun Arda Turan a minti na 76.

Da wannan nasara Atletico a karon farko ta yi nasara a gidan Real a wasanni a jere.

Kafin wasan kocin Atletico Diego Simeone na ganin da wuy kungiyarsa ta iya kare kofin na La Liga saboda 'yan wasansa biyar da suka bar kungiyar a lokacin sayar da 'yan wasa.