Ahly ta dau Super cup bayan casa Zamalek

Image caption Ana buga kusan duk wasannin Masar ba 'yan kallo tun bayan abun da ya auku a Port Said a 2012, inda 'yan kallo fiye da 70 suka mutu

Kungiyar Al Ahly ta cinye Zamalek da bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ta lashe Super Cup gabanin fara wasannin kakar Firimiyar Masar ta bana.

An dai tashi wasan tsakanin zakarun kasar ta Masar ne canjaras babu ci, inda kai tsaye aka tafi bugun fanareti bayan cikar minti na 90.

Kaftin din Zamalek Ibrahim Salah ne ya baras da bugunsa na fanareti, lamarin da ya bai wa Al-ahly nasara.

Za a fara gasar Firimiyar kasar ne a yau litinin ba tare da halartar 'yan kallo ba, kamar yadda aka haramta musu kallon daukacin gasar a bara.

Sai dai ba kamar a bara da aka raba kungiyoyin zuwa rukuni biyu ba, a bana za a buga wasannin ne kamar yadda aka saba cikin rukuni guda.