Nicolas Anelka ya koma taka leda a India

Image caption Za a fara buga gasar ta makwanni 10 a watan gobe, da nufin bunkasa karbuwar kwallon kafa a Indiya.

Tsohon dan wasan gaban Faransa Nicolas Anelka zai buga wa kulob din Mumbai City yayin bude gasar Super League ta India a bana.

Anelka wanda tsohon dan wasan Arsenal da Real Madrid ne, West Brom ta sallame shi a watan Maris bayan ta same shi da aikata ba daidai ba.

Tafiyarsa daga West Brom ta biyo bayan haramta masa wasanni da cin tararsa da Hukumar kwallon kafan Ingila ta yi saboda yin wata sara da ke bayyana kin jinin yahudawa a lokacin da ake buga wasa.

Dan wasan mai shekaru 35 ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa "Ina farin cikin shiga Mumbai City FC kuma na zaku da shiga gasar Super League ta Indiya."

Bafaranshen wanda kungiyoyin da ya buga wa wasa sun hadar da Chelsea da Man City ya ce "Hazikan 'yan wasan duniya da fitattun 'yan wasan Indiya za su kara wa gasar armashi a bana."

Shahararrun 'yan wasa a gasar Kwallon kafa ta Indiya

Tsohon fitaccen dan wasan Brazil Zico- Koci a kungiyar FC Goa Tsohon dan wasan tsakiyar Ingila Peter Reid- Kocin Mumbai City Tsohon dan wasan gaba na Ipswich Michael Chopra- kulob din Kerala Blasters Tsohon dan wasan gaban Faransa David Trezeguet- kungiyar FC Pune City Tsohon dan wasan baya na Spaniya Joan Capdevila- kungiyar North East United Tsohon dan wasan tsakiyar Arsenal Freddie Ljungberg Tsohon dan wasan gaban Liverpool Luis Garcia- kungiyar Atletico de Kolkata