Yau za a yi wasannin Zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Real Madrid ce ke rike da Kofin gasar Zakarun Turan

A yau za a fafata wasanni goma sha daya na gasar cin kofin Zakarun Turai a kasashe daban-daban na Turai.

Ga yadda wasannin za su gudana; Olympiakos Piraeus da Atlético Madrid.

Juventus da Malmö FF; Liverpool da Ludogorets ; Real Madrid da FC Basel.

Monaco da Bayer Leverkusen ; Benfica da Zenit ; Galatasaray da Anderlecht ; Borussia Dortmund da Arsenal.