'Ina kishin ganin Man U a Gasar Zakaru'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karon farko kenan da Kocin Liverpool, Brenden Rodgers zai jagoranci wata kungiya zuwa gasar

Kaftin din Liverpool Steven Gerrard ya ce ya ji kishin ganin Manchester United da Chelsea suna fafatawa a gasar zakarun Turai, ba tare da kungiyarsa ba, tsawon shekaru biyar.

Liverpool dai ta samu shiga gasar zakarun Turai a karon farko tun cikin 2009, inda za ta karbi bakuncin kungiyar Ludogorets Razgrad ta Bulgeriya a gida.

Gerrard wanda ya lashe gasar a shekara ta 2005 ya ce "Na rika jin wani abu kamar kishi da kyashi ganin babu mu a gasar."

Ya ce ya yi ta kulafucin ganin kungiyarsa ta je gasar Zakarun Turai, ya ce babu dan wasan da ba ya son jin taken gasar.

Chelsea ta lashe Gasar Zakarun Turai, inda Manchester United kuma ta zo ta biyu a cikin shekaru biyar din da Liverpool ta kasa zuwa.

Gerrar ya ce ya yi farin ciki don kuwa a bana dai kwalliya ta biya kudin sabulu, ya ce sun cancanci yabo saboda aiki tukuru da suka yi.

Kungiyar wadda ta lashe Gasar Zakarun Turai sau biyar na cikin rukuni daya da Real Madrid da kuma FC Basel.