Super Eagles na cikin tsaka mai wuya

Image caption Tattaunawa ta ci tura sakamakon gwagwamaryar neman shugabancin Hukumar NFF

Nijeriya na bukatar nada wani koci a kurarren lokaci kafin zuwa wasan samun shiga gasar cin kofin Afirka da za ta yi da Sudan a watan gobe, saboda rikicin da ya dabaibaye Hukumar kwallon kafa ta kasar.

Yanzu dai akwai gurbi a kujerar kocin Super Eagles, bayan karewar yarjejeniyar wasanni biyu da Stephen Keshi ya sanya hannu.

Sai dai Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta ce ba za ta tattauna da kowanne koci ba, sai bayan ta kammala nada sabon shugaba.

Hukumar za ta gana a karshen wannan mako don sanya ranar gudanar da zabe.

Super Eagles dai ta fara wasannin samun shiga gasar cin kofin Afirka da kafar hagu a karkashin jagorancin Keshi, inda ta sha kashi a hannun Congo ta kuma yi canjaras da Afirka ta kudu yanzu haka tana matsayi na uku a rukunin A.

Nijeriya dai tana cikin matsin lamba don samun nasara a wasan da za ta yi a gidan Sudan, ranar 10 ko 11 ga wata mai kamawa.

Stephen Keshi mai shekaru 52, wanda ba a sabunta kwanturaginsa ba bayan kammala gasar cin kofin duniya a Brazil, an ba shi jagorancin kungiyar na wucin gadi a lokacin da Ministan wasannin kasar ya sa baki.