Aston Villa ta kara kwanturagin Hutton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya buga wa Aston Villa wasanni 31 a kakar 2011 zuwa 2012

Dan wasan baya na kungiyar Aston Villa, Alan Hutton ya sanya hannu kan wata sabuwar kwanturagin shekaru uku, watanni bakwai bayan an fada masa cewa abincinsa ya kare a kungiyar.

Dan wasan bai buga wasa ba fiye da shekaru biyu, kafin a sake kiran shi a wannan mako.

Kocin kungiyar, Paul Lambert ya fada a watan Fabrairu cewa matsalolin sun sa mai yiwuwa Alan Hutton ya hakura da buga wa kungiyar wasa.

Dan wasan na Scotland, mai shekaru 29, ya je zaman aro a kungiyoyi da suka hadar da Nottingham Forest da Real Mallorca da kuma Bolton.

Hutton, wanda kwanturaginsa za ta kare a karshen wannan kaka, ya je Villa daga Tottenham a kan kudin da ba a bayyana adadinsu ba cikin watan Satumban 2011.