'United ba za ta iya sayen 'yan wasanmu ba'

Pep Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Guardiola ya ce United ba ta da kudin da za ta iya sayen 'yan kwallon Munich

Pep Gurdialo ya ce kungiyar Manchester United ba za ta iya daukar 'yan kwallo Bayern Munich domin su ci gaba da buga tamaula a Old Trafford ba.

Kocin Munich ya ce babu wani dan wasansa da zai bar Allianz Arena, domin United ba ta da kudin da za ta iya sayen dan kwallonsa.

United ta kashe sama da fam miliyan 150, ciki har da sayen Angel Di Maria daga Real Madrid a matsayinsa na dan wasa mafi tsada a tarihin kwallon kafar Ingila.

Guardiola wanda Louis van Gaal ya horas dashi a matsayin dan wasa a Barcelona ya ce kasa samun tikitin shiga gasar zakarun Turai da United ta yi na nuna rashin tabbacin kwallon kafa.

"Kowanne mako sai ka zage damtse ka kuma shirya sosai, ba ka yi kokari a mintuna 45 ba, sauran mintuna ka kasa katabus ba".