Mu kara bai wa Welbeck lokaci - Wenger

Danny Welbeck Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Welbeck a karawar da ya kasa zura kwallo a ragar Borussia Dortmund

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya roki magoya bayan Arsenal da su kara hakuri da Danny Welbeck a kan rashin zura kwallo a raga a wasanni biyu da ya bugawa kulob din.

Welbeck mai sheakaru 23, dan kwallon Ingila, ya kasa zura kwallo a ragar City a wasan da suka buga da Borussia Dortmund a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Talata.

Dan wasan ya koma Arsenal ne kan kudi fam miliyan 16 daga United bayan da kulob din ya dauko Radamel Falcao aro daga kungiyar Monaco ta Faransa.

Wenger ya ce, "Ya kamata mu kara hakuri mu kuma bashi lokaci ya saba buga tamaula da 'yan wasanmu".

Arsenal ta tashi wasa 2-2 da Manchester City a gasar Premier, inda Borussia Dortmund ta doke Arsenal 2-0 a gasar cin kofin zakarun Turai.

Welbeck ya zura kwallaye biyu a raga a lokacin da Ingila ta doke Switzerland da ci 2-0 a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ranar 8 ga watan Satumba.