Lambert ya tsawaita kwantiraginsa da Villa

Paul Lambert
Bayanan hoto,

Kocin ya fara gasar Premier bana da kafar dama

Kocin Aston Villa Paul Lambert ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar tsawon shekaru hudu, har zuwa karshen kakar wasanni ta 2018.

Villa ta fara gasar Premier bana da kafar dama, inda har yanzu ba a doke ta ba a gasar, bayan buga wasanni mako hudu.

Lambert, mai shekaru 45, ya karbi ragamar horas da Villa a shekarar 2012, kuma bai taka rawar gani ba a bara, inda Villa ta kare a mataki na 15 a teburin Premier.

Kocin ya kuma nada tsohon dan kwallon Manchester United Roy Keane a matsayin mataimakinsa a farkon kakar wasan bana.

Villa tana matsayi na biyu a teburin Premier bana, inda take biye wa Chelsea wadda take mataki na daya.