CAF ta dakatar da Birori shekaru biyu

CAF
Bayanan hoto,

Tun farko CAF ta kori Rwanda daga buga wasannin share fagen shiga kofin Nahiyar Afirka

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta dakatar da dan kwallon Rwanda Dady Birori buga wasanni na tsawon shekaru biyu.

CAF ta samu dan kwallon ne da laifin mallakar fasfo biyu dauke da sunaye da shekaru daban daban.

Birori yana amfani da fasfo din Rwanda, haka kuma yana da fasfo din Jamhuriyar Congo inda yake amsa sunan Etekiama Agiti Tady kuma shekarun sun bambanta.

Dan wasan yana buga wa kulob din AS Vita na Rwanda tamaula inda yake amsa sunan Tady.

CAF ta ce Rwanda ta san dan kwallon yana amfani da fasfo biyu, amma ta yi masa rijista kuma ya buga mata wasa.