Solskjaer ya bar kocin Cardiff City

Ole Gunnar Solskjaer
Bayanan hoto,

Kocin ya kwashe watanni 9 yana jagorancin Cardiff City

Ole Gunnar Solskjaer ya sauka daga matsayin kocin Cardiff City bayan watanni 9 da ya jagoranci kungiyar.

An ba da sanarwar ajiye aikin Solskjaer mai shekaru 41 ne, bayan kammala tattaunawar shugaban kulob din Mehmet Dalman da kocin.

Cardiff tana matsayi na 17 a gasar cin kofin Championship bayan ta yi rashin nasarar wasanni uku, ciki har da doke ta da Middlesbrough ta yi da ci 1-0 da lashe ta da Norwich ta yi da ci 4-2.

An bai wa tsoffin 'yan wasan kulub din Danny Gabbidon da Scott Young matsayin kociyan rikon kwarya.

Tun kafin a fidda sanarwar ajiye aikin Solskjer, BBC ta hakikance cewa kocin Dundee Paul Hartley mai shekaru 37, ya ki amincewa da tayin horas da Cardiff City.

Ana hasashen cewa Tony Pulis tsohon kocin Crystal Palace da Stoke City ne zai gaji kujerar kocin kungiyar, ko da yake, ya ce babu wanda ya tuntube shi dangane da aikin.