Everton ta casa Wolfsburg da ci 4-1

Asalin hoton, Getty
Rabon Everton da gasar Europa tun shekarar 2010
Kulob din Everton ya doke Wolfsburg ta Jamus da ci 4-1 a gasar cin kofin zakarun Turai wato Europa da suka fafata a Godison Park ranar Alhamis.
Everton ta fara zura kwallo a raga bayan da Ricardo Rodriguez ya ci kansu da kansa a mintuna na 15 da fara tamaula, kafin Seamus Coleman ya kara kwallo ta biyu da kai daf a tafi hutu.
Bayan an dawo daga hutu ne Everton ta samu fenariti, inda Leighton Baines ya buga ta kuma shiga raga.
Dan wasan Everton Kevin Mirallas ne ya zura kwallo ta hudu muntuna biyu a tashi wasa, yayin da Ricardo Rodriguez ya zare kwallo daya daf a tashi wasa a bugun tazara.
Ga sakamakon wasannin da aka buga:
Partizan Belgrade 0 - 0 Tottenham FC Red Bull Salzburg 2 - 2 Celtic Apollon Limassol 3 - 2 FC Zürich Borussia Mönchengladbach 1 - 1 Villarreal Rio Ave 0 - 3 Dynamo Kiev Steaua Bucharest 6 - 0 Aalborg BK Fiorentina 3 - 0 Guingamp PAOK Salonika 6 - 1 Dinamo Minsk Legia Warsaw 1 - 0 KSC Lokeren Metalist Kharkiv 1 - 2 Trabzonspor Club Brugge 0 - 0 Torino
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti daya da BBC Safe 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,14
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 20/01/2021 wanda Sani Aliyu da Nabeela Mukhtar Uba su ka karanto.