Fulham ta raba gari da kocinta Magath

Felix Magath
Bayanan hoto,

Tun a watan Fabrairu kocin ya fara horas da Fulham

Fulham ta sallami kocinta Felix Magath sakamakon rashin kokarin kungiyar a gasar cin kofin Championship.

Tuni kuma ta nada Kit Symons a matsayin kocin rikon kwarya don jagorantar kulob din da ke wasa a Craven Cottage.

Magath, mai shekaru 61, ya fara horas da Fulham a watan Fabrairu, inda ya kasa hana kulob din fadowa daga gasar cin kofin Premier.

Fulham tana mataki na karshe a teburin Championship inda take da maki daya a wasanni bakwai da ta buga.

Magath shi ne koci na uku da kulob din ya sallama bayan Martin Jol da Rene Meulensteen, kuma karkashinsa ne kulob din ya bar Premier bayan shekaru 13 a gasar.